Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da biyan mafi karancin albashi na N70,000, wanda aka kara daga N40,000 da gwamnatinsa ke biya a baya, matakin ya janyo cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya amma gwamnan ya ce duba da faduwar darajar kudin kasar – Naira da kuma tsadar rayuwa, ya sanya dole ne a fara gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.Ya yi magana ne a gidan Talabijin na Channels Television.