RMC Hausa
LIVE Radio

EFCC YAHAYYA BELLO

*EFCC DA YAHAYYA BELLO*

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, EFCC ta kai samame tare da yi wa gidan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ƙawanya, a Abuja, babban birnin ƙasar.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, sai dai babu wani cikakken bayani a kan yadda ta kaya, amma dama a watan Maris ɗin da ya gabata EFFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a kotu kan zarginsa da halatta kuɗin haram har naira biliyan 84.
Mai taimaka wa tsohon gwamnan kan watsa labarai ya yi tur da lamarin yana mai neman Shugaba Bola Tinubu ya saka baki wajen jan hankalin EFCC kan abin lamarin.
Rahotanni sun ce gwamnan Kogi mai ci, Usman Ododo ya ziyarci Yahaya Bellon bayan samamen da EFCC ta kai masa.
Jaridar trt Africa ta wallafa.

RMC HAUSA TIMES

Post a Comment

Previous Post Next Post