*SANARWAR! SANARWA!! SANARWA!!!*
*ARC AHMAD MUSA DANGIWA LITERARY FOUNDATION*
*Tare da haɗin guiwar*
*ƘUNGIYAR MARUBUTAN JIHAR KATSINA (KMK)
Na farin cikin gayyatar marubuta da manazarta da masu ruwa da tsaki akan hulɗar rubutu, domin halartar taron bita da tattaunawa akan gasar gajerun labarai da gidauniyar *ƊANGIWA* ta saka a shekarar 2020 da 2022 tare da ƙaddamar da sabuwar gasar gajerun labarai ta 2024.
Za a yi wannan taro kamar haka;
RANA:- Lahadi (21-04-2024)
LOKACI:- Karfe goma na safe (10:00am)
WURI:- PLBC (Abba Saude House dake shataletalen titin filin jirgin sama na Malam Ummaru Musa Yar'adua da zai kai ka/ki kwaɗo).
Allah ya bada ikon zuwa ameen.