AN GABATAR DA TARON JIN RA'AYI DA MASU RUWA DA TSAKI NA GASAR GAJERUN LABARAI TA ARC. AHMAD MUSA DANGIWA TA 2022 DA 2023 TARE DA KADDAMAR DA GASAR 2024
A ranar 21 ga watan Afrilun 2024 ne aka gabatar da taron bita da tattaunawa da Manazarta da Marubuta domin jin ra'ayoyinsu kana yadda gasar gajerun Labarai ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa ta gudana a shekarun baya, an bayar da dama ga Marubutan da manazarta su bayyana duk wani abu da suke ji game da gasar da kuma bada shawarwari a Inda suke ganin akwai matsala ko kuma inda za a inganta.
Taron ya samu halartar masana daga Jami'o'i mabambanta da kuma Marubuta daga garuruwa mabambanta.
A wajen taron an yi bitar litattan da gasar tavsamar da suka hada da Muhalli, Sutura da Daukar Jinka tare da bayyana irin muhimmancin da litattafan suke da shi ga al'umma, sannan an tattauna Nasarorin da gasar ta samu tare da bada shawarwari kan yadda za a kara inganta gasar a mataki na gaba.
Kazalika Sakataren kwamitin shirya gasar Abdulrahman Aliyu ya yi bayanin kaddamar da Maudu'in da gasar ta bana (2024) zata kalla, Inda ya bayyana cewa a bana batun da za a yi rubutu kansa shi ne 'BURI' Inda za a bukaci marubuta da su samar da labarai da aka gina su kan buri na rayuwa. Shi wannan maudu'in zai taimakawa marubutan da su bayyana damuwarsu da kansu, sannan taken zai taimakawa manazarta wajen gano irin bukatuwa da kuma makomar al'ummar Hausawa ta daga bakinsu.
Batun wani sabon salo ne da aka samar da zai zama wata hanya ta gano irin cigaban da ke fuskantar al'ummarmu dangane da kimiyya da siyasa da sauran fasahohi na Duniya.
Daga karshe an bayyana ranar 4 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a saki gasar domin a fara ta.