RMC Hausa
LIVE Radio

BAKAR ASHANA 03

*BAƘAR ASHANA*

*Safnah Aliyu jawabi*
(His Noor)

Page 4•5

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*

Follow the PERFECT WRITERS ASSOCIATION channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vad1bE05a249vbEcab0r


Cikin r dare ta fara ihun bayanta na ciwo tun yana ɗaukar abin wasa har dai abu ya yi tsanani cikin sauri ya tayar da maƙota mata suka shiga gidan cikin yardar Allah ta haifi 'ya'yanta guda biyu mace da namiji, ban da hamdala babu abin da yake tun da ya fara jiyo kukan jarirai, ita kuwa tsabar mamaki kasa furta ko kalma ɗaya ta yi, sai yanzu kalamansa ke sake dawowa kanta, 'za ki daina ganin al'adarki, kuma cikinki zai kumbura' innalillahi wa inna ilaihi raju'un kawai take maimaitawa. Bayan an gyara mata jiki da sauran abin da ba za a rasa ba aka bata abinci ta ci kan ka ce me tuni bacci ya yi awan gaba da ita. Da yake da ma cikin dare ta sauka, ganin tayi barci yasa  ya yi musu godiya ya raka su har ƙofar gidansu sannan ya dawo. Haska fuskar yaran ya yi ya ga suna ta barci abin gwanin sha'awa, murmushi ya yi, ya fita daga ɗakin ya ɗauro alwala, a dakalin  ɗakin ya shimfiɗa sallayar sa ya shiga jero nafila yana miƙa godiyarsa ga Allah mahaliccin kowa da komai. Tun asuban farko jarirai suka hau tsala ihu, cikin barcin ta taji ihun su har kanta, tashi ta yi tana tsaki, kallon yaran  cike da tsana. Ta sake gyara kwanciyarta tana cewa "Ai kuwa kuka da shi za ku koma inda kuka fito dan kuwa ba'a bukatar ku anan aikin banza aikin wufi mtsss"Jin kukan na su yaƙi ƙarewa yasa ya yi sallama ya kwashe sallayar ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama ganin ta kwance tana batci har da minshari  yafi komai bashi mamaki, sauke ajiyar zuciya ya yi yace,
"Tawan dan Allah ki taimaka ki tashi ki shayar da waɗanan yaran kin ga  kuka suke  cikin dare wanda hakan bai dace ba dan Allah"
"Kai har ka san Allah munafiki algungumi maƙaryaci, kai kasan Allah? to Wallàhi bara ka ji sai ka yi da ka sanin wanan abin da kayi, kuma ka rubuta ka aje. Maganar shayarwa kuma kai kanka kasan cewa ka yi ƙarya Wallahi. Can ka tafi ka nema musu abincin da za su ci, amma ni Wallahi idan za su mutu ba zan shayar dasu ko ruwa ba zan basu ba bare kuma abin da ke jiki na, a halin yanzu nafi tsanar su akan mutuwa ta"
Tana kaiwa nan ta gyara kwanciyar ta ta koma bacci. Gaba ɗaya Najib ji ya yi  duniya tana juya masa ga wani ciwon kai da ya yi masa dirar miƙiya jin wa'anan kalamai daga bakin Hedaya, ganin yadda yaran suke tsala kuka ai kuwa babu shiri hawaye suka fara zarya a kuncinsa, miƙa hannu ya yi ya ɗauki macen wadda ta kasance itace Husaina ya rungume yana jin so da ƙaunar ta yana ratsa jinin sa, sake ɗaukar Hassan ya yi ya daura saman ɗayar kafaɗar sa, jijjiga su yake yana musu karatun Alkur'ani a kunne har suka koma bacci. Hamdala ya yi yana godiya ga Allah da ya sa suka koma bacci cikin ƙankanin lokaci. Samun wuri ya yi a ƙasan ɗakin yana tunanin makomar yaransa, share hawayan daya zubo masa ya yi ya ce "Allah ka san da ni kuma ka fi kowa sanin halin da na ke ciki Allah ka sassauta mata zuciya a kaina da kuma 'ya'yanta. Da haka bacci yayi awan gaba da shi. Kiran sallar assalatu ta farka ganinsa kwance ya sa ta ji wani abu ya tsaya mata a maƙogoro duk da sanyin da ake hakan bai hana ta yin gumi ba dan kuwa gumi ne a fuskar ta har tana ɗiga. Ta fita daga ɗakin ta ɗebo ruwa a randar da ke tsakiyar gidan ta watsa masa a jiki tana cewa,
"Wallahi tunda ka saka katanga tsakani na da burina ni Hidaya na yi maka alƙawarin ka yi bankwana da zaman lafiya a rayuwarka. Ka tsumayi zuwan tashin hankali wanda sai kayi da ka sanin zuwan ka duniya. Sai na shayar da kai azaba mai raɗaɗi wannan alƙawarin na ne".
"Alhamdullah tunda ba alƙawarin Allah ba ne ba, kuma kar ki mance ni musulmi ne kuma na yarda da ƙaddarar Allah a kaina. Saboda haka babu abin da zance ki fasa daga cikin ƙudirinki a kaina. Sai dai ki sani Allah yana kallon ki kuma yana sauraron ki, za ki koma gare shi wata rana kuma zai tambaye ki, ina fata za ki tanadi amsar da za ki ba shi a kan amanar da ya damƙa miki ina miki fatan alkairi"
"Mtsss mutum kamar na Allah to Wallàhi yau duk wa'azinka babu wani mazaunin da za su samu a zuciyata, babu abin da zai hana ni cikar buri na ba kai ba hatta wa'annan ƙaddararrun 'ya'yan"
Ta samu wuri ta kwanta, shi kuwa murhu ya nufa ya haɗa wuta sannan ya ɗora musu ruwan zafin wanka ita da jarirai kafin jama'a su fara shigowa. Yana gamawa ya nufi 'family house' ɗinsu cike da murna don kuwa ji yake kamar ba shi da wata matsala da zarar ya tuna da yaran sai yaji sanyi na ratsa jini da jijiyarsa. A Zaune ya tarar da mahaifiyarsa tana azkar kamar yadda ta sa ba. Ya samu wuri ya zauna har sai da ta idar, ta kalle shi cike da so da ƙaunar ɗan nata so irin wanda a cikin idanuwan uwa kawai ake iya ganin irin sa. Murmushi ya yi mata yana shafe kai bayan sun gaisa ta ce,
"Fatan an sauka lafiya me aka samu?"
Da mamaki yace, "Waya sanar dake Mimah ta?"
"Farin cikin da ke kwance saman fuskar ka ya fi karfin farin cikin samun kuɗi ko kuma wani ƙalƙyali na duniya, irin wannan farin cikin na gani ranar da ka zo duniya a fuskar mahaifinka dan haka sanar da ni wani iri aka samu"
Zancen mahaifiyar tasa ya ji ya mance komai dangane da maganar Hidaya, sunkuyar da kai ya yi yace "'Yan biyu mace da namiji Mimah"
"Alhamdullah Allah ya raya su cikin sunna"
Miƙewa ta yi ta sanar da mahaifinsa da kuwa sauran 'yan uwa na gidan, kan ka ce me gida ya cika da jama'a sai barka ake masa. Gaba ɗaya kunya ta gama yi masa bargo burin sa kawai ya bar gidan ya tafi gun 'ya'yansa. Sai dai kuma murmushin da ke kan fuskar mahaifiyarsa kawai ya isa tsayar da shi a wurin tsawon shekaru muddun ba za su gushe daga kan fuskarta ba. Ruwan zam-zam ta miƙa masa da dabino tace ya ba su sannan ya yi musu huɗuba. "Mimah sunanki zan saka dana Abba in sha Allah"
"A'a ni a zuciya ta akwai sunan da nake so ka saka musu"
"Faɗi ina jinki Mimahta" 
"Ita macan ka saka mata sunan  mahifiyar matarka, shi kuma namijin ka sanya masa Abdullah"
"Mimah wane ne  Abdullah?"
"Ba na son yawan tambaya ka saka masa sunan daga baya zan yi maka bayani dalla-dallah." 
Ya shiga ɗakinta ya yi tagumi, sosai hankalinsa ya yi mugun tashi ganin yadda lokaci ɗaya annurin fuskarta suka ɓace kamar ma ba su taɓa wanzuwa ba. Wane ne wannan Abdullah ɗin wanda ambaton sunansa ya sa mahaifiyata shiga wannan halin, menene haɗin su da Mimahta? Akwai bukatar na bincika, dafe ƙafaɗarsa mahaifin sa ya yi yana cewa,
"Karka damu ka tafi gidan in sha Allah da kanta za ta ba ka labari, amma yanzu ka tafi gun matarka"
"Shi ke nan Abba nagode"

2

Zuwansa gida ke da wuya ya same ta kwance saman gado ta yi ƙwalliya abinta. Fuskarta kuwa yadda ka san hadari, Allah cikin ikonSa yaran sun yi bacci kafin ya dawo. Ta kalle shi sannan ta ce, "Ni kam sai yanzu ma nake ƙare wa halittarka kallo, anya ba asiri ka yi mini ba kuwa? Gaskiya wannan lamarin da sake, don kuwa Idanuwana a buɗe wallahi ba zan auri irinka ba. Ya kamata ka farka daga baccin da kake yi, ka sani yanzu wannan asirin ya karye.  Ganina ya dawo tas, ko kusa ba ka dace da ni ba, Allah sai ka sake ni!"

"Wannan maganar ai kuma idan kika duba ba da ni kike ba, kina magana ne kai-tsaye da Ubangijin daya halicce ni. Don haka kina iya faɗar duk abin da kika ga dama. Ni dai alfarmar da nake so ki min ita ce; ki shayar da yaran nan da zarar sun farka ba don ni ba, a'a sai dai Sayyidina rasulil..." Tsawar da ta daka masa ya sa ya yi gum, ba tare da ya kai aya ba.

"Wai kai sai yaushe za ka daina haɗa ni da Allah cikin maganarka? Ok yanzu na fahimci abin da kake nufi aljannar ma baƙin ciki kake min ko? idan ka haɗa ni da Allah na yi maka abu, ban yi ba, sai Allah ya yi fushi da ni ko? To wallahi burinka ba zai taɓa cika ba, Na daɗe da ɓaro jirginka. Wallahi duk ranar da ka sake haɗa ni da Allah sai na yi maka lahani".

Jin kamar ana sallama ya sa ta yi saurin hayewa gado, ta lulluɓe kanta da zanin gado sannan ta share kwalliyar fuskarta. Gaba ɗaya kasa amsa sallamar ya yi ganin abin da take yi. Sai da aka sake yin sallamar sannan ya amsa. Da fara'arsa ya tarbe su, ƙanwar mahaifiyarta ce sai kuma ƙanwar mahaifinta. Daga nan kuma ya fita domin sayo musu abinci, kasantuwar babu wanda zai yi girki tunda hakimar na jigo, shi kuma bai samu zama ba. Abin mamaki suna shiga ta fashe da kuka har da shashsheƙa kamar wadda aka wuni ana jibgar ta. Gwaggo Rabi ta rungume ta, tana cewa, "Mene ne kuma na kukan bayan aikin gama ya gama da haka kowa yake farawa."

"Au wai saboda sakarci kukan haihuwar take? Bayan ga 'ya'yanki suna kwance a kusa da ke kina jin ɗumin jikinsu, ai kuka kuma ya ƙare yarinya."

"Umma Ƙarama ba kukan da nake ke nan ba, fushin da yake da ni ya fi komai tayar mini da hankali"

"Fushi kuma to laifin me kike yi masa?"

"Umma ƙarama wai shi bai so na haifi mace ba saboda duk maza yake da burin na haifa masa, shi ya sa ya ce: Wai karda na yardar na shayar masa da 'ya'yansa."

Tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka, Umma Ƙarama da yake tana da zafin rai da kuma saurin hawa, aikuwa nan ta fara zazzaga masifa. Shi kuwa bawan Allah da murnarsa ya dawo cikin gidan riƙe da ledar ruwa da lemon ƙwalba. Jin yadda take ta zazzaga masifa ya sa abin ya ɗaure masa kai. Ya yi shiru yana sauraron ta bai ce mata komai ba har ta gama. Kodayake sam bai fahimci ma ina zancan nata ya dosa ba. Buƙatar ma-je-hajji salla, shi dai kawai ya za a shayar da yaran ne a gabansa. Ƙanwar mahaifinta ce ta yi gyarar murya tana cewa,

"Kai yanzu Najib abin da ka yi, ya yi daidai ke nan? Kar ka manta Allah shi ne yake bayar da wannan ba mutun ba. Kuma shi ne yake da ikon bayar da duk jinsin da ya yi niyya, mene ne aibun mace? Idan ba a haihuwar mace kai ta ina za ka fito duniyar har ka nemi ɗaga wa matarka hankali? Wai don ta haifa maka mace kuma kake iƙirarin kar ta shayar maka da 'ya'ya, idan ka yi haka ka yi daidai ke nan? kar ka mance ita ce ta ɗauke su a cikinta har na tsawon wata tara yanzu kuma ka ce kar ta shayar da su? ba ka tunanin akwai haƙƙinsu su 'ya'yan a kanka ban da ma na mahaifiyar tasu?"

Gumi kawai yake sharewa don kuwa ji ya yi kamar an rufe masa bakinsa. Mamaki ne ya yi wa tunaninsa mamayar bazata. Sanadin hakan ya hana ƙwaƙwalwarsa sarrafa zantukan da za su iya ba shi kariya bisa wannan tuhumar da ya ma gaza gane tushenta. "Don Allah ku rinka kai zuciya nesa idan har lamari irin wannan ya kasance. Yin haka fa kamar butulci ne ga Mahalicci, ina roƙon ka don Allah ka bar ta ta shayar da 'ya'yanta cikin salama. To wai ma ina laifi, mace da namiji ne fa"

Gyaran murya ya yi, ya ce "Na yi kuskure kuma ina mai ɗaukar miki alƙawarin ba zan sake maimaita irin shi ba don Allah ku min aikin gafara"
"Ai babu komai tunda ka gane cewar ka yi kuskure."
Ana cikin haka Husaina ta tsala ihu ɗaukar ta Umma ƙarama ta yi ta miƙa mata ita tana cewa,
"Me kike jira? Maza ba wa 'yarki gudan jininki nono ta sha. Idan kika ga haka yanzu wata can yake nema, yana jiran ki masa laifi wanda bai taka kara ya karye ba ya sako mana ke ki dawo gida. Maza ba ta ta sha ko babu komai za ta ji tausayin ki"

Wani irin baƙin ciki ne ya mamaye mata zuciya lokacin da Umma ƙarama ta sanya wa Husaina nono a baki ta fara sha. Hawaye masu zafi take zubarwa tsabar baƙin ciki, tsanar da take wa 'ya'yan ta ji ta ƙaru ɗari bisa ɗari.

Shi kuwa ganin haka ya sa ya yi hamdala yana mai godiya ga Allah da ya yi masa wannan taimakon, domin kuwa idan ba shi ba babu wanda zai iya yi masa wannan agajin gaggawar.
"Alhamdullahi" Ya ambata a can ƙasan maƙoshinsa.

Ganin yadda yake sauke ajiyar zuciya ya sa ta banka masa harara tana masa alamar mu zuba ni da kai. Karaf sai a kan idon  Gwaggo Rabi, mamaki da tararrabi ne suka cika mata zuciya. Yadda ya raƙuɓe wuri ɗaya ne ya sa ta ce. "Yawwa Najib idan babu matsala mu je mana mu yi shawara kan sunan da za a sanya wa yaran naka ko?"

Fita suka yi daga gidan gaba ɗaya, ta kalle shi sannan ta ce, "Kar ka ɓoye min komai don ni ba yarinya ba ce mene ne yake faruwa tsakanin ka da Hidaya?"

Ya duƙar da kansa ƙasa bai ma san ta ina zai fara yi mata jawabi ba. Ita kuwa ganin hakan ya sa ta cigaba da magana tana cewa,
"Najib ni ma tamkar mahaifiya nake a gare ka, kada ka kalli cewar matarka ce kawai 'yata. Ina so ka saki jikinka, ka faɗa mini duk abin da yake faruwa.
Nan fa ya kwashe komai ya faɗa mata tun daga farkon auransu har zuwa rana mai kamar ta yau.

Ban da salati da sallalami babu abin da Gwaggo Rabi take tsabar yadda abin ya ba ta mamaki.

Ba shi hakuri ta yi tare da alƙawarin in sha Allah tana zuwa gida za ta sanar da mahaifinta abin da ke faruwa.
"Gwaggo ina godiya sosai da kika fahimce ni, amma ina neman alfarma don Allah kar a faɗa wa Abba domin ina tsoron hukuncin da zai yanke mata. Idan da so samu ne tunda babu abin da Kaka take don Allah a roƙa min ita ta zo nan ta zauna da ita har zuwa arba'in, lokacin Yaran sun ɗan fara ƙwari don Allah Gwaggo"

Post a Comment

Previous Post Next Post