'Jami'in Kwatsam Ya Harbe Kansa A Banɗaki A Kano'
Wani jami’in hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa, Abdulwahab Magaji, dake aiki a babban birnin tarayya, ya harbe kansa har lahira a gidansa da ke Garin Centre a Kano, lamarin ya faru a yau Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa iyalan mamacin sun bayyana cewa Marigayin ya harbe kansa ne da bindiga, kuma suka sanar da hukumar 'yan sanda, lamarin da ya sa jami’an ‘yan sanda suka ziyarci inda lamarin ya faru, kuma bayan an garzaya da mamacin zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Mai magana da yawun rundunar Kwastam ta kasa Abdullahi Maiwada ya tabbatar wa manema labarai mutuwar jami'in Kwatsam Abdulwahab Magaji, ya ce an gano gawarsa ne a banɗaki a gidansa tare da bindiga ƙirar pumb action, a jihar Kano, "jami'in yana aiki ne a Abuja amma a Kano lamarin ya faru.
Sai dai zuwa yanzu ana binciken musababbin rasuwarsa, ba zamu iya faɗa ko shi ne ya kashe kansa ba ko a'a, har sai abinda bincike ya tabbatar". In ji Abdullahi Maiwada.