RMC Hausa
LIVE Radio

BAKAR ASHANA 2

*BAƘAR ASHANA*

*Safnah Aliyu jawabi*
(His Noor)

Page 2•3

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*


Washegari tun da sanyin safiya ya tafi wurin Iro wanda ya kasance abokinsa tun na yarinta ya ce, "Iro magana na zo mu yi da kai dan Allah"
"Wai Me ya sa kake mini haka ne Najib, na faɗa maka ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba cewar ni da kai ba abokan juna ba ne ba, kai ɗan uwa na ne kuma ni ma ɗan uwan ka ne, dan haka kawai ka faɗa mini mece ce matsalar ka."
Share hawayan sa ya yi ya ce, 
"Rancan kuɗi nake so ka ba ni dan Allah"
"Mtsssss na ma ɗauka wani abin ne ya faru a gida fa, kuɗi kamar nawa ke nan?"
"Nawa ake sayar da ƙaramin maraƙi?"
"E to ana samu kamar dubu sittin da biyar haka"
"To dubu sittin da biyar za ka ara mini dan Allah da zarar na tafi kasuwa zan ba ka ka ji"
"Amma dai to bara na ba ka kar ka ce na shiga rayuwar ka ni kuwa da na tambaye ka abin da za ka yi da kuɗin nan Najibu?"
"Dan Allah kar ka tambaye ni Iro kawai ka ba ni idan kana da shi".
"Shi ke nan ina zuwa."
Ko da Iro ya ba shi kuɗin sai da ya zauna a wurin ya ci abinci sannan ya tashi ya nufi gida. A zaune ya same ta  ta yi ƙwalliya, kallon ta yake zuciyarsa cike da so da ƙaunarta don kuwa Hidaya in dai kyau ne duk ƙauyensu babu macen da ta kai ta, ita ɗin fara ce sosai irin mai ɗaukar ido ɗin nan ga ta da dara-daran idanuwa hancinta kuwa har baka, bakinta madaidaici murmushi ta sakar masa tana cewa.
"Ya dai na ga ka tsaya a ƙofa?"
"Ke dai bari a gajiye nake ne" ya faɗa tare da yamutsa fuska.
"Fatan dai an yi nasara?" Ta tambaya da sauri.
"Eh an yi nasara sai dai ba yadda muke so ba gaskiya sai dai ki yi hakuri kamar nan da sati biyu haka sai mu sake jarabawa ƙila mu samu wadda tafi wannan girma." Ya faɗa tare da laluba aljihunsa alamar akwai abin da yake nema.
"Me kake nufi?" Ta tambaya tare da tsare shi da idanuwanta masu ɗaukar hankalinsa. Miƙa mata kuɗin ya yi yana dafe kansa. Wani irin tsalle ta yi ta ɗare jikinsa tana masa godiya. Haka suka kasance cikin wannan daren sun rayashi cikin farinciki. Washegarin ranar tun da sanyin safiya ta nufi gidan ƙawarta Raliya da murna suka rungume juna, lokacin da ta faɗa mata abin da ke faruwa kuma a tare suka yi shewa.
"Raliya in sha Allah daga nan zuwa wata uku duk kuɗin da nake buƙata sun haɗu daga nan kuma zan nuna masa asalin kalata ta hanyar gana masa azaba iri daban-daban har sai ya gaji dan kansa ya rabu da ni".
"Kin min daidai, wannan shi ne kawai hanyar da za mu bi dan ganin burinmu ya cika"
"Ke fa ina labari?"
"Hmmn! Ki bari kawai Wallahi ba na samun komai a gurinsa"
"Ban gane ba ki samu ba?"
"Ya kike so nayi Hidaya? wannan mutumin ba kamar mijinki ba ne ba, shi kam duk abin da zan yi masa wallàhi ko tankani ba ya yi tsabar mugunta ma sai dare ya yi kuma ya ce ga shi nan"
"Kam bala'i Wallahi ina mai tabbatar miki kin yi sake a wannan zamanin wake irin wannan auren ai sai sakarya. Malama idan za ki dawo hankalinki  Wallahi ki dawo dan ba zama kirga musu 'ya'ya muka zo ba".
"Insha Allah zan canza wata dabarar".
"Shi ne dai kawai mafita"
"Kin ga bari na tafi ba na so ya dawo gida bai gan ni ba"
"Shi kenan sai na zo."
Da haka suka rabu ta koma gida komawarta ke da wuya ta ji cikinta na wani irin juyawa, kwanciya ta yi amma ina can kuma sai amai kamar za ta amayar da kayan cikinta, tana cikin haka ya shigo gidan a rikice ya isa gare ta yana tambayarta abin da ya same ta. Nuna masa cikinta kawai take dan kuwa zuwa lokacin har ta fara galabaita. Cikin hanzari ya nufi ƙaramin asibitin da yake cikin garin da ita. ruwa aka saka mata saboda jikinta babu ƙwari, zuwa ya yi ya faɗawa iyayansa  da kuma nata iyayan sannan ya koma asibiti. Ganin Dr ya fito daga ɗakin ya sa suka sake yin musabaha sannan ya ce, "Ina ta yaka murna matarka tana ɗauke da juna biyu na tsawan sati biyar yanzu"Hamdala ya yi wa Ubangijinsa sannan ya yi godiya ga likitan, har likitan zai tafi ya tsayar da shi gabaɗaya jikinsa a mace yake dan kuwa ya yi imani tsaf za ta salwantar da cikin nan tun da ba ƙaunarsa take ba. Bayani ya yi wa likitan kan irin magungunan da za a ba ta ta yadda ba za ta fahimci tana da juna biyu ba har sai cikin ya kai matakin da ba za ta iya cirewa ba, sosai likitan ya yi mamaki amma kuma sanin yadda komai na duniyar yake canzawa hakan ya sa ya rubuta masa magani ya ba shi. Sai kusan maraice aka sallame su suka koma gida.Bayan ya idar da Sallar isha'i ya zo ya zauna kusa da ita, saka hannunsa ya yi cikin nata yana cewa. 
"Tawan akwai abin da zan faɗa miki dan Allah kar ki ɗaga hankalinki ki tsaya ki ji abin da zan faɗa miki, kuma na yi miki alƙawarin duk abin da zai same ki wala na daɗi ko kuma cuta babu shakka ina nan tare da ke babu gudu babu ja da baya, ba komai nake son faɗa miki ba sai ciwon da likita ya sanar da ni wanda shi ne dalilin da ya sa kika yi wannan rashin lafiyar. Kallon sa take zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi. Ganin yadda ya tsorata ta ya sa ya yi gyaran murya yana ce wa, "Duk kan mu haƙuri za mu yi mu miƙawa Allah lamuranmu dan kuwa duk ya fi mu sanin abin da yake daidai, likita cewa ya yi kina ɗauke da ciwon hanta wanda kuma ya yi tsanani sosai ta yadda idan har ba a ɗauki  mataki mai tsauri ba babu shakka za ki rinƙa kumbura haka ma cikinki saboda ciwon ya yi tsanani"
Ban da zufa babu abin da take ga hawaye sai gangara suke kamar an buɗe fanfo, share mata hawayan ya yi ya ce,
"kuma ya ce daga yanzu har zuwa lokacin da za ki warke ba za ki sake ganin al'adar ki ba har sai kin warke kin dawo kamar da yanzu ni abin da ke damuna shi ne idan mutane suka ji kina da wannan ciwo gudunki za su riƙa yi ni kaina saboda ƙaunar da nake miki ne ya sa kawai nake tare da ke kuma kin ga dole a faɗawa iyayanki ko?"
Cikin sauri ta rungume shi tana girgiza kai ta ce,  "A'a don Allah ka yi mini rai kar ka faɗa wa kowa wannan maganar don Allah, Wallahi gudu na za su yi kuma ni ba na so. Yanzu a ina za mu samu maganin wannan ciwo dan kuwa ina da buri a rayuwata ka taimaka mini"
"Daina kuka in shaa Allah zan rufa miki asiri har mu samu ki rabu da wannan ciwon in shaa Allah"Da haka ya samu ya ƙwantar mata da hankali daga tunanin ciki gare ta kuma ta daina shiga cikin jama'a kullum tana gida kwance, ganin yadda cikinta ke girma ya sa ta ƙara tsorata da lamarin ciwon ko da mutane sun zo wurinta sai dai ta ce a ce ta fita ba ta nan. Shi kuwa hakan ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba sai dai kuma bai ɓoyewa mahaifiyarta da kuma kakarta halin da ake ciki ba, dan kuwa wannan shawara ma daga gun kakarta ya samu. Kullum cikin bacci da kuma cin abinci take babu dare babu rana cikinta kuwa sai girma yake girma na ban mamaki kullum cikin kuka take tana cewa za ta mutu ne ba tare da ta cika burin rayuwarta ba. Murmushi kawai yake dan kuwa ya san nan ba da jimawa ba cikin zai shiga watan haihuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post