Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta kama wata tankar iskar gas da aka cika ta da buhunan tabar wiwi guda 511.
Hukumar ta ce buhunan tabar wiwin da nauyinsu ya kai kilogiram 4,752, an dauko su ne daga Jihar Ondo zuwa Abuja domin rarraba ta ga mabuƙata.
Jami’an NDLEA sun kuma ta gano wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta ƙasa da ƙasa a sassan Najeriya.
Akalla mambobin kungiyar dillalan kwayoyin da ke da alaƙa da kasashen Afirka ta Kudu da kuma ƙasar Thailand guda biyar ne aka kama a jihohin Legas, Abia da Anambra.