Wani ya kirani a waya a akan wani korafi.
Mai kira: hello ina magana da PRO Sadiq ne ?
Ni: Eh PRO Sadiq.
Sai muka gaisa. Bayan gaisuwa.
Mai kira: PRO an kama ɗan uwa akan laifin da bai aikata ba.
Ni: A ina ? Kuma mene ya faru ?
Sai yayi mun bayani cewa, Dan uwan shi na saye da sayar wa sai wasu samari suka kawo mai kaya sai ya siya. Kwatsam sai ga yaran tare da yan sanda anzo an kama shi wai ya sayi kayan sata. Toh PRO shi fa bashi yayi satan nan ba kawo mai kaya akayi kuma ya siya ya za ayi a kamashi ?
Sai nace masa ranka shi dade, shin ko kasan cewa siyan kayan sata laifi ne babba ? Sai ya kara da cewa bafa shi ya sato ba.
SIYAN KAYAN SATA LAIFI NE BABBA. DON HAKA A DUK LOKACIN DA WANI YA KAWO MUKU KAYA DON KU SIYA. KUYI KOKARIN BINCIKEN ASALIN WAƊAN NAN KAYAN DON GUJEWA SIYAN KAYAN SATA.
KUMA MU SANI CEWA "RASHIN SANIN DOKA BAYA ZAMA UZURI"
Aliyu Abubakar Sadiq
Pro katsina police command
Rmc Hausa times