RMC Hausa
LIVE Radio

AN DAKATAR DA BBC A NIJER

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan Watsa Labarai na Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou, ta ce an dakatar da watsa duka shirye-shiryen BBC kai-tsaye da na abokan hulɗarta na ƙasar da suka haɗa da R&M da Saraounia da Anfani har tsawon wata uku.
Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne saboda yadda kafar ta BBC ta watsa bayanan 'ƙarya' waɗanda za su iya kawo matsala ga kwanciyar hankali a ƙasar, da kuma dakushe karsashin dakarun kasar.

RMCHAUSA1
 
Talla
RMCHAUSA1

Post a Comment

Previous Post Next Post