Tchani ya zama Damisar takarda - Martani daga Rarara
Mawaƙin jam'iyyar APC Dauda Kahutu Rarara ya sake mayar da martani ga Shugaban Mulkin Sojin Nijar Abdurrahman Tchani.
Rarara dai ya tara Malamai Dubu Guda inda suka gabatar da saukar karatun alƙur'ani mai girma.
Ya ce, sun yi hakan ne don neman Allah ya taimaki Najeriya sannan ya rusa shirin da Tchani ke yi da Bokaye.
A makon da ya gabata ne DW ta ruwaito Shugaban Nijar din ya nemi taimakon Ƴan Bori da Bokaye na Afrika kan dambarwarsa da wasu ƙasashe ciki har da Najeriya.
Sai dai Rarara ya ce, wannan ya nuna tsantsar rashin ƙwarewa da rashin dogaro ga Allah, a don haka ya nemi Ƴan Nijar su dage da addu'a domin Tchani ya kama hanyar jefa su a rami.
Rarara ya ƙara da cewa da mamaki a ce Soja ya koma neman ɗaukin Bokaye waɗanda ba za su iya tsinana masa komai ba.
Rararan ya ce, yanzu ta bayyana a zahiri Tchani ya zama Damisar Takarda.
Rarara ya ƙara da cewa, irin ƙaunar da ya ke yiwa ƴan Nijar ta sa ya ke damuwa da abin da ke faruwa a ƙasar.
A ƙarshe ya rufe da cewa, yana tunasar da Tchani ya sani cewa babu abin dogaro sai Allah, kuma shi kaɗai ne mai bada kariya amma Bokaye ba za su iya yiwa ko da kansu magani ba.
Me za ku ce a kan hakan?
RMCHAUSA1
Daga shafin freedom radio.📻🛫