RMC Hausa
LIVE Radio

FURSUNONI SUN SAMU 'YANCI A KATSINA

Babban Jojin Katsina ya bada belin fursunoni 91, ya saki 4 a yunkurin rage cunkoso a gidajen gyaran hali a fadin jihar. 

Da yake jawabi yayin shirin, Mai Shari’a Danladi ya bayyana cewa an ba da belin ne bisa shawarwarin kwamitin rage cunkoson gidajen gyaran hali, bisa dalilai daban-daban.  

Wasu daga cikin fursunonin da aka sake sun samu wannan dama ne saboda yawan shekarunsu, tsawon zamansu a gidan yari, ko kuma matsalolin lafiya.  

Ya shawarci wadanda aka saki da su kasance masu bin doka da oda, yana gargadi cewa irin wannan dama ba lallai ta sake samuwa ba idan suka sake aikata laifi.
An samo daga katsina post.

Randawa Media Concept.

Post a Comment

Previous Post Next Post