Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa jiharsa ta shiga wani sabon mataki na bunƙasa titunan karkara domin kawo sauƙi ga zirga-zirga da harkokin kasuwanci.
Yayin kaddamar da wasu daga cikin titunan, ya ce gwamnati ta samu goyon bayan RAAMP da ƙungiyoyin ci gaba bayan nazarin matsalolin al’ummomin karkara.
Ya ce inganta hanyoyi zai taimaka wa manoma wajen fitar da kayayyakinsu, tare da karfafa haɗin kai tsakanin al’umma da cibiyoyin kasuwa da sauran ayyuka.
A gefe guda, ya bukaci Sarkin Bauchi da ya kula da sabbin masarautun da aka kirkira, don tabbatar da ingantacciyar shugabanci a yankunan.
Hanyoyin da aka ƙaddamar a yau sun haɗa da:
(1) Ningi-Dagu Rd
(2) Gadar Maiwa-Zakara
(3) Katsinawa-Polchi-Maraban Liman Katagum Rd
(4) Nabordo-Jama'a-Doka Rd
(5) Dot-Dado-Baraza Rd
(6) Maraban Dajin Rd
RMC HAUSA
Category
labarai