RMC Hausa
LIVE Radio

ƳANCIN RAYUWA

*SHUGABAN ƘASA BOLA AHMED TINIBU*

*Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinibu ya yi bayani ga ƴan ƙasar kamar haka*

Ku tuna cewa na soke tafiyar da na yi niyar zuwa taron kolin G20 a Afirka ta Kudu domin in daidaita ayyukan tsaro a gida.

Godiya ga kokarin jami'an tsaronmu a cikin ƴan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka sace a Eruku, Jihar Kwara.

Ina kuma farin ciki da cewa an ceto dalibai 51 daga cikin daliban Makarantar Katolika da suka bata a Jihar Niger.

Ina sa ido sosai kan yanayin tsaro a duk fadin Ƙasar kuma ina mai ci gaba da samun labarai na cigaba daga rundunar.

Bari in bayyana karara: Ba zan yi kasa a gwiwa ba. Kowanne dan Najeriya, a kowace jiha, yana da 'yancin samun tsaro - kuma a karkashin kulawa, za mu kare wannan kasa da kuma kare mutanenmu.

RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post