RMC Hausa
LIVE Radio

GWAMNAN KATSINA YA JE TA'AZIYA

*GWAMNAN KATSINA YA KAI ZIYARAR TA'AZIYAR SHEIKH DAHIRU BAUCHI*

 A ranar Lahadi, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranci wata babbar tawaga da ta hada da malamai, iyayen kasa da wasu jami’an gwamnatin Katsina zuwa garin Bauchi don yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Babban Malamin Addinin Musulunci a Nigeria, Shaikh Dahiru Usman Bauchi wanda Allah yayiwa rasuwa satin da ya gabata. 

A madadin gwamnati da mutanen jihar Katsina, gwamna Dikko Radda ya mika sakon gaisuwa ga iyalai, gwamnati da alummar Nigeria kan rashin Shaikh Dahiru Bauchi, wanda gwamnan ya bayyana a matsayin Malamin, Uba kuma Shugaba ga alummar Nigeria dama wasu sassan kasashen Africa. Ya bayyana rayuwar malam a matsayin abun koyi ga alumma saboda irin yadda rayuwa tayi tsayi kuma ta amfani alummar musulmi. 

A madadin iyalan marigayi, Sayyadi Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, yayi godiya ga maigirma gwamna da tawagarsa kan ziyara da ta’aziyyarsa. Ya kuma bayyana yadda marigayi yake son jihar Katsina saboda kararsu, zumuncinsu da kuma son addininsu. Ya kuma bayyana cewa ahalin Malam zasu cigaba da wannan zumunci da Katsina da mutanenta har abada Insha Allah.

Tawagar tayi adduar rahama ga marigayi Shaikh Dahiru Usman tare da fatan Allah ya yafe kura kuransa kuma sa yana aljanna tare da Manzon Allah SAW. 

Tawagar gwamna ta hada da ministan gidaje, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, Kakakin Majalisar Jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahya, Kwamishinan Harkokin Addini, Hon Dabai, Chief of Staff, Hon Abdulkadir Mamman Nasir, PPS, Hon Abdullahi Turaji, Shugaban Izala na jihar Katsina da kuma Babban Limamin Masallacin Sarki, da sauran malamai da iyayen kasa. 

RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post