RMC Hausa
LIVE Radio

MAI RABA ALKAIRI SANI YA GINA ASIBITI

Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Sabon Asibiti da Hon. Sani Ɗanlami Ya Gina a Unguwar Maƙera

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya ƙaddamar da katafariyar asibitin da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Hon. Sani Aliyu Ɗanlami, ya gina a Unguwar Maƙera da ke cikin mazabar Shinkafi B.

A yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Radda ya jinjinawa Hon. Ɗanlami bisa wannan gagarumar gudummuwa da ya bayar ga al’umma. Ya ce sabon asibitin zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta kiwon lafiya, rage cunkoso a sauran cibiyoyin lafiya.

Shima Hon. Sani Ɗanlami, a jawabinsa, ya gode wa Gwamna Radda bisa girmamawar da ya nuna wajen amincewa da ƙaddamar da aikin. Ya yi alkawarin cigaba da wakilci na gari, tare da ƙara kawo ayyukan da za su amfani jama’a a yankin Katsina ta Tsakiya.

Hon. Ɗanlami ya kuma nuna farin cikinsa ga jama’ar da suka halarci bikin, yana mai cewa goyon bayan su ne ke ƙara masa ƙarfi wajen aiwatar da ayyukan ci gaba.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post