*AMURUKA TA ZARE KANTA DAGA SHIGA FADAN ISRA'ILA*
Idan Isra'ila ta kaiwa Iran hari babu ruwanmu a ciki - Amurka
A yayin da Isra'ila ke nazarin yadda za ta mayar da martani kan harin da Iran ta kai a karshen mako, Amurka ta bayyana cewa babu ruwanta idan har kasar ta zabi daukar fansa ta hanyar soji.