An kori wasu ɗalibai ƴan Najeriya daga makaranta tare da ba su umarnin barin Birtaniya saboda gazawa wajen biyan kuɗin makaranta sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar tasu naira.
Hakan dai ya faru ne a Jami'ar Teesside, wadda ta dakatar da ɗaliban daga shiga aji saboda rashin biyan kuɗin makaranta a kan lokaci.