Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta soke sarakuna biyar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙira.
Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis ɗin nan.
A jawabin da ya gabatar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Lawal Hussaini, ya ce majalisar ta soke dukkan "masarauti biyar da aka ƙirƙira inda za a koma tsarin Masarauta guda ɗaya kamar yadda yake a baya."
Masarautun da aka soke su ne: Birnin Kano, Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye.