*RUWAN SAMA YA RUGUJE GIDAJE*
Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro dan shekara 7 a Tsohon Garin Nangere da ke karamar hukumar Nangere a jihar Yobe.
Rahotanni na nuni da cewa mutane 20 ne suka samu munanan raunuka, yayin da gidaje da shaguna kusan 50 suka ruguje sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.