RMC Hausa
LIVE Radio

AN DAKATAR DA KWAMISHINA

Gwamnan Jigawa ya dakatar da kwamishinansa kan zargin lalata da matar aure

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya dakatar da kwamishinsa na ma'aikatar ayyuka na musamman, Auwalu Danladi Sankara bisa zarginsa da lalata da wata matar aure.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, ta ce matakin na zuwa ne bayan zargin da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi masa kan aikata ma sha'a.

Ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya da kuma kare martabar aikin jihar.

"Mun ɗauki duka zarge-zargen da muhimmanci kuma za mu yi bincike da nufin fito da gaskiya domin duka ƴan jihar Jigawa su gani," in ji sakataren gwamnatin jihar.

Ya kuma ce an ɗauki matakin dakatar da kwamishinan ne domin yin sahihin bincike da kuma yin adalci ga kowane ɓangare.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce abin kunya ne abin da ake zargin kwamishinan da aikatawa kuma cin fuska gare ta.

Tuni kuma gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti mai mambobi huɗu waɗanda za su yi bincike da kuma gabatar da rahoto cikin mako biyu kacal.
RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post