GWAMNA ABBA KABIR YUSUF YA KAI ZIYARA GA DALIBAN JIHAR KANO A INDIA
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci daliban jihar Kano da ke karo karatu a Jami’ar Sharda, India, a wani bangare na kokarinsa na tallafa wa matasa da karfafa bangaren ilimi.
Ziyarar, wadda ta kasance cike da alamar kulawa da kishin al’umma, ta bawa daliban kwarin gwiwa yayin da Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta ilimi a gida da waje. Ya ce:
"Ku ne wakilan jihar Kano a kasashen duniya. Gwamnatinmu za ta ci gaba da mara muku baya domin ganin kun cimma burin ku. Muna alfahari da ku."
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen samar da damarmaki ga matasa domin su zama jagororin gobe. Wannan ziyara ta kara tabbatar da cewa gwamnatin Kano tana daukar ilimi a matsayin ginshikin cigaban al'umma.
Daliban sun jinjinawa kokarin Gwamnan, suna mai bayyana godiya da yadda yake kulawa da walwalarsu da burinsu na samun ingantacciyar ilimi a matakin duniya.
RMCHAUSA1