Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi wa majalisar zartarwarsa garambawul, inda ya sauke Sakataren Gwamnati Dr. Abdullahi Baffa Bichi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati Shehu Wada Sagagi da kuma wasu kwamishinoni biyar.
Daraktan watsa labarai na gwamnatin jihar Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, wadda ta ce an kuma yi wa kwamishinoni da dama sauyin ma’aikatu.
A cewar sanarwar, “Gwamna Yusuf dauki wannan matakin ne da aka dade ana jira don ba da damar gudanar da aiki mai inganci wanda zai bai wa al'ummar jihar Kano damar ci gaba da sharbar romon dimokuradiyya.”
RMCHAUSA1
Talla
SHUKA A IDON MAKWARWA
Nabila Shehu Binji