Babban Limamin Babban Masallacin Lagos, Sheikh Ridhwan Jamiu ya ce Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Ahmad Tinubu bai ba su kunya ba.
Liman Ridhwan ya fadi hakan ne a yayin Sallar Juma'a ta jiya, wadda Shugaban Tinubun ya halarta a birnin na Ikko.
Limamin ya kuma tabbatar wa da Shugaban Kasar jajircewar al'ummar Musulmai wajen yi masa addu'o'i a lokacin da yake shugabantar ƙasar.
RMCHAUSA1