*WTC/GGASS KABOMO TA YI BIKIN KAFA KUNGIYA NA SHEKARU 30*
Shugabanni kungiyar cigaban Makarantar WTC/GGASS Kabomo sun gudanar da gagarumin taronsu a katsina,na cika shekaru talatin da kafuwar kungiyar tsofaffin daliban.
Kungiyar ta tallafawa tsoffin daliban da jari don fara sana'ar dogaro da Kai,haka ma Hajiya Jamila Ahmad Rufa'i shugabar kungiyar ta jaddada aniyarsu ta ciyar da 'ya'yan kungiyar gaba tare da gina rijiyar burtsatse da gyara wasu a cikin Makarantar tare da bada kyautar mota bus ga daliban Makarantar don daukar dalibai zuwa asibiti.
Bugu da Kari kungiyar tsoffin daliban ta gyara kofofi da tagogin Makarantar tare da kawata masallacin da daliban Makarantar ke ibada.
Taron ya tashi cikin farinciki da jin dadin sake haduwar tsoffin daliban a shekaru masu tsawo.
Isah Randawa
RMCHAUSA1