Gidauniyar Gwagware ta bayar da gudunmuwar kayayyakin yakin neman zabe ga yan takarakarin shugabannin kananan hukumomi da mataimakan su na kananan hukumomi (34) dake jihar Katsina.
A ranar laraba 22-01-2025 shugaban Gidauniyar Alh. Yusuf Ali Musawa ya jagoranci taron bada gudunmuwat ga yan takarkarin a ofishin Gidauniyar dake hanyar Daura cikin garin Katsina.
Da yake bayyana abubuwan da Gidauniyar ta shirya badawa ga yan takarkarin shugaban Gidauniyar Alh. Yusuf Ali Musawa ya bayyana cewa " fastoci ne guda dubu da za'a bada kowace karamar hukuma.
Tare da banoni wanda za'a manna a cikin garuruwan da suke domin kara neman al'umma, ya bayyana wannan gudunmuwa ce wadda Gidauniyar ta bayar wanda akwai sauran abubuwan da zasu biyo baya.
Daga karshe yayi kira ga yan takarkarin da su tashi tsaye wurin neman al'umma domin kare martabar jamiyyar Apc da gwamna Mal Dikko Umar Radda.
Da suke gabatar da jawabin su na godiya wasu daga cikin yan takarkarin shugabannin kananan hukumomin da suka tofa albarkacin bakin su sun yi godiya ga Gidauniyar ta Gwagware bisa basu wannan gudunmuwa.
Taron ya samu halartar mambobin Gidauniyar, daukacin yan takarkarin shugabannin kananan hukumomin da mataimakan su.
RMCHAUSA1