Gidauniya Aliko Dangote Foundation ta jaddada aniyarta na cigaba da ciyar da al’ummar jihar Kano abincin bude baki tunda farkon Ramadan har zuwa karshensa.
Bayanin hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake rabon abincin a wannan rana, ta bakin wakilin gidauniyar ta Dangote na kafafan yada labarai Tukur S Tukur, inda ya bayyana cewa su na iya kokarinsu na ganin sun sauke nauyin da gidauniyar ta dora mu su na tabbatar da adalcin a ya yin rabon abincin.
Tukur S Tukur ya kara da cewa gidauniyar ta Aliko Dangote a bana ta kara kayata abincin da dake bayarwa fiye da na bara, ba ya ga Biredi mai kyau da inganci da ake bayarwa tare da ruwan roba da lemo a kowanne kunshin abincin.
Sannan ya godewa kafafan yada labarai bisa hadin kai da suke bawa kungiyar wajan sanar da duniya ayyukan da suke gudanarwa.