RMC Hausa
LIVE Radio

GWAMNA RADDA YA JE JAJE

*GWAMNA RADDA YA KAI ZIYARAR JAJE GA JAMI'AN TSARO NA CWC*

Gwamna Radda Ya Kai Ziyara Ga Jami’an Tsaro na CWC da Suka Jikkata a Asibitin FMC Katsina

Da yammacin yau, Gwamna Dikko Umaru Radda ya kai ziyara Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina domin duba wasu jami’an Community Watch Corps (CWC) da suka jikkata sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Marhaba da ke karamar hukumar Matazu. Gwamnan ya kuma yi wa wasu marasa lafiya sallama da addu’o’i na samun lafiya.

Gwamna Radda ya tabbatar wa da jami’an da suka jikkata da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar, tare da yabawa da jarumtar da suka nuna yayin gudanar da aikinsu. Ya ce: “Sadaukarwarku ba za ta taba mantuwa ba.”

A cikin tawagar da suka raka gwamnan akwai Alhaji Kabiru Bature Sarkin Alhazai, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina; Sarkin Kuraye, Alhaji Usman Darda’u; wasu dagatai da kuma Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Harkokin Tsaro da Community Watch, Alhaji Yusuf Ibrahim Safana, wanda ya jagoranci yawon zagayen asibitin.

Ziyarar na nuni da jajircewar Gwamna Radda wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Katsina da kuma mutanen da ke bayar da gudummawa wajen kare su.

RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post