*ZAKARUN GASAR FA CUP*
Crystal Palace ta lashe kofin FA Cup na Ingila, bayan da ta doke Manchester City da ci ɗaya mai ban haushi a wasan ƙarshe na gasar da aka buga yau Asabar 17 ga Mayu 2025.
Ɗan wasan gaba, Eberechi Oluchi Eze, wanda haifaffen Ingila mai tsatson Nijeriya shi ne ya ci ƙwallon guda da ta ba su nasara. An buga wasan ne a babban filin wasan Ingila na Wembley, wanda ke birnin London.
Wannan ne karo na farko da Crystal Palace ta ci wani babban kofi a tarihinta na tsawon shekaru 119 da kafuwa a matsayin ƙungiyar ƙwallon ƙwararru.
Ita kuwa Man City, wannan ne karo na farko a ƙarƙashin koci Pep Guardiola, da take ƙare kakar wasa ba tare da ɗaga kofi ko guda ba.
RMC HAUSA