Rundunar Sojin Kasa Ta Yiwa Kakakinta Karin Girma Zuwa Kanar
Babban Hafsan Sojin Kasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ɗaga mukamin Mukaddashiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Sojojin Kasa, Appolonia Anele, zuwa matsayi na Kanal a wani biki da aka gudanar a Abuja.
COAS ya yaba da jajircewarta da kwarewarta, tare da jaddada muhimmancin amincewar jama’a da kuma sadarwa ta gaskiya wajen nasarar ayyukan soja.
Ya kuma buƙaci Daraktan ta ci gaba da bin ƙa’idojin aiki, ladabi da gaskiya a hulɗa da jama’a.
Kanal Anele ta godewa manyan hafsoshi bisa kyakkyawan jagoranci da goyon bayan da suka ba ta .
RMC HAUSA
Category
labarai