*Burkina faso tayi ƙorafi kan sojin Najeriya*
Burkina Faso ta ce jirgin soja dauke da sojojin Najeriya 11 ya karya dokar sararin samaniyarta
Gwamnatin Burkina Faso ta ce wani jirgin soja dauke da sojojin Najeriya 11 ya karya dokar amfani da sararin samaniyarta.
A cikin wata sanarwa da shugabanta, Assimi Goïta, ya sanyawa hannu, gwamnatin kasar ta bayyana cewa wani jirgin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya yi saukar gaggawa a garin Bobo Dioulasso a ranar Litinin, bayan “wani yanayi na gaggawa a cikin jirgi” lokacin da yake aiki a cikin sararin samaniyar kasar.
“An fara gudanar da bincike nan take daga hukumomin Burkina Faso kuma sakamakon ya nuna cewa jirgin bai samu izinin wucewa ta sararin samaniyar Burkina Faso ba,” in ji sanarwar.
RMC HAUSA
Category
labarai