RMC Hausa
LIVE Radio

MINISTA A GIDAN KURKUKU

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya ranar Jumma'a ta tura tsohon Ministan Ƙwadago Chris Ngige gidan kurkuku da ke Kuje.
Kotun ta ɗauki matakin ne bayan hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Mariam Hassan bisa tuhume-tuhume takwas da suka jiɓanci cin hanci da rashawa na kimanin N2.2bn.
EFCC tana zargin Ngige da aikata laifukan a lokacin da yake minista ƙarƙashin gwamnatin marigayi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, musamman a lokacin da yake kula da hukumar bayar da tallafi ta Nijeriya (NSITF).
Tsohon ministan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa a kansu.
Mai shari'a Mariam ta ɗage shari'ar zuwa Litinin domin sauraron buƙatar neman belinsa, kana ta bayar da umarni a tsare shi a gidan yarin Kuje zuwa ranar.

RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post