RMC Hausa
LIVE Radio

SAIRA YA ZAMA GWARZO

Tashar Saira Movies ta zama tasha ta huɗu da aka fi kallo a shafin YouTube a Nijeriya a shekarar 2025.

Kamfanin YouTube ne ya fitar da jerin tashoshi 10 da aka fi kallo a shekarar 2025 inda duk sauran taran na kudancin ƙasar ne, in ban da Saira Movies.

Saira Movies, mallakin shahararren darakta nan Aminu Ahmad Saira, ta yi shuhura ne wajen nuna fitaccen shirinta na “Labarina” wanda aka daɗe ana nuna shi, inda a duk sati mutane aƙalla miliyan ɗaya suke kallonsa a tashar.

RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post