RMC Hausa
LIVE Radio

BAKAR ASHANA 01 NISHADI

*BAƘAR ASHANA*

*Safnah Aliyu jawabi*
(His Noor)

Page 1

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*

Zaune take a tsakar gida, a gaban murhu, hayaƙi ya turnuƙe ta yadda ba kowa zai lura da mutum a wurin ba. Tari take babu ƙaƙƙautawa saboda ta haɗu da ɗanyen itace; shi bai kama ba,  kuma bai mutu ba. Haka ta yi ta ƙoƙarin iza wutar har dai ta yi dace ta kama. Miƙewarta ta yi daidai da ɓallewar tekun hawaye daga kogin idonta ya gangaro kuncinta. Ta ɗebo ruwa a wata ƙaramar tukunya ta ɗora a wutar sannan ta shiga ɗaki. Shigarta kenan aka fara sallama, fitowa ta yi tana amsa sallamar.  Wani ƙaramin yaro ne ya shigo hannunsa ɗauke da baƙar leda. Bayan ya gaishe ta ya miƙa mata ledar sannan ya ce, 
"Ga shi, cewa ya yi na kawo miki shi ma zai dawo nan da ɗan lokaci."
Ta miƙa hannu ta karɓa sannan ta ce da shi,
"Shi ke nan, je ka." 
Yana fita ta buɗe ledar, tsaki ta yi tare da ashariya kana ta soma mita, 
"Allah ya yi wadan naka ya lalace....yanzu duk cewar da yake na haɗa wuta yau kayan daɗi zai shigo mana da shi ashe wannan zai kawo?" Ta ƙarasa maganar tana kallon garin rogon fuska a yatsine tamkar wadda ta ga kashi. 

"Wallahi za ka dawo ka same ni, wannan wahalar da na sha wurin hura wutar ba za ta tashi a banza ba. Babu abin da zan girka yau a gidan nan, mtss! Ni ke nan kullum cikin cin abincin Inyamurai? Wallahi ba za ta taɓa saɓuwa ba, wai bindiga a ruwa." Zalamammiyar zuciyar tata ke ƙara rura mata wutar gajiya da tsanar yanayin da mijin nata ke ciki. Ta nufi kan murhun a fusace, ta sa ƙafa ta yi fatali da tukunyar. Komai ya baje a dandagaryar ƙasa, kamar an yi ɓari. A lokaci guda kuma ruwan ya zube baki ɗaya a kan murhun.
"Mtssss! Aikin banza kawai." 
Ta faɗa tana huci tare da hararar murhun tamkar shi ya yi mata laifin. Shi kuwa da sallamarsa ya shigo, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin farin ciki mara misaltuwa, ganin ba ta tsakar gidan ya sa ya yi sallama ya shige ɗakinsu. 

A zaune ya same ta tana karkaɗe ƙafa. Da tattausan murmushi a kan faffaɗa kuma zagayayyar fuskarsa mai annuri  ya ce, "Gimbiya a yi mini aikin gafara wallahi wani abokin cinikayya ne ya zo kuma babu yadda za a yi na taho ba mu gama daidaitawa ba shi ya sa na makara. Gimbiyata ɗan yi min murmushi mana ko na ji daɗi a rai na!"
Wani irin yaƙe ta yi mai kama da kuka sannan ta miƙe ta ɗauko wannan ledar tana zuwa ta juye masa a jiki, gabaɗaya kasa magana ya yi domin kuwa garin rogon har cikin idanuwansa, murza idanuwansa yake cikin sauri, wani yaji-yaji yake ji mai azabar gaske.
"Kai har ka isa ka ce za ka wulaƙanta ni? Da ma na san tun da na gan ni a duniyar nan matsayin matarka na san cewa kawai rako mata na yi.  Babu abin da zan samu sai baƙin ciki da tulin takaici. Bari ka ji na faɗa maka, Wallahi ba zan ci garin rogo ba, kuma babu shakka duk inda abinci yake sai ka nemo ka kawo mini! Idan kuma ba haka ba ka shirya tunkarar masifa da tashin hankali, don sai ka yi rigar sakawa da su ka ji na faɗa maka!"
Tsagwaron mamaki da takaici ne ya sanya shi kasa buɗe baki ya yi magana. Hawaye na safa da marwa a kan baƙin kundiƙukinsa. Jiki a sanyaye ya miƙa mata ledar da ke hannunsa ya ce, "Wannan shi ne abin da na yi miki alƙawarin zan kawo miki gida, wanda kika watsa mini kuma shi ne wanda nake so na jiƙa na sha kafin na kwanta. Yanzu kin zubar da shi, kin wajabta mini sake fita neman abin da zan ci, a madadin zama domin warware gajiyar da na kwaso a fafutukar sauke nauyin da yake kaina! Hmmm! Sai na dawo."
"Mtsssss! Idan ka ga dama ka kwana a can ina ruwana." Ta faɗa cike da tsiwa. A  tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ya matso inda take ya ce,
"Wai ko dai canza mini ke aka yi ne? Domin Hidaya ɗina ba za ta taɓa kasancewa haka ba. Idan kuma wani laifin na yi miki ki faɗa mini don Allah. Ni kuma na yi miki alƙawarin zan daina in dai hakan zai faranta ranki gimbiyata."
"Dan Allah malam ka cika mini kunne da wasu surutanka na banza. Ka ga, idan wannan guntuwar rabin kazar taka da ka kawo mini ita ce ta sa kake jin cewar ka kai matsayin da za ka tsaya a gabana kana magana sai na mayar maka da tsiyarka ga ta nan."
"A'a, yi hakuri yanzu zan tafi ki ɗauka ki ci don Allah ba na so kina zama da yunwa."
"Idan a gidanka ne wallahi yunwa har sai ta nemi zama ajalina, shi ya sa tuni na yanke shawarar rabuwa da kai tun kan wankin hula ya kai ni dare. Abin da ba ka sani ba shi ne, Wallahi a gare  ni auranka tamkar auran ƙaddara ne, wanda tuni Allah ya rubuta faruwarsa. Amma ga wani ƙarin albishir yadda aka rubuta kasancewata da kai haka kuma aka rubuta rabuwata da kai dan haka ka shirya."
A wannan karon bai iya ɓoye mamakin da ya dabaibaye  zuciyarsa ba. Hakan sai da ya bayyana raɗau a kan fuskarsa, cikin sanyin murya ya fara mai da kata martani.
"Idan da can ba ki so na me ya sa kika amince kika aure ni?".
"Allah ya kawo mu lokacin da nake jira don na faɗa maka dalilin auranka. A yanzu tsawon wata bakwai da auranka, amma ji nake kamar na shekara dubu. Dalilina shi ne ganin mahaifinka ya fi kowa kuɗi da kuma yawan shanu a garin nan, hakan ya sa na yi tunanin na aure ka ko babu komai tunda ya tsufa nan ba da jimawa ba zai mutu. Kasantuwar kai ne ɗansa na fari kuma namiji ɗaya tilo, ka ga ke nan dukiya za ta dawo hannunka. Amma kash, abin mamaki tsoho sai ƙara lafiya yake babu zancen mutuwa! Ka ga kuwa gara na tafi dan kuwa ba ka da wata mamora. Ƙarin takaicin ma kuma wai kai mai gaskiya ba za ka tafi ka ɗauki ko da guda ɗaya ba ne ka sayar! Shi ya sa na ɗora ɗamarar barin gidanka ko ta halin ya ya".
Ban da zufa babu abin da ke karyo masa, idanuwansa kuwa sun yi ja alamar ɓacin rai. Ya kalle ta zuciyarsa na masa raɗaɗi da suya.
"Dalilinki ke nan dama?"
"Tabbas!" Ta tabbatar masa.
"Idan kuma ka mini alƙawarin canzawa ni kuma zan nuna maka ƙauna fiye da tunaninka." Ta yi furucin da wata manufar, yayin da shi kuma ya fahimci wani abin daban.
"Shi ke nan, in sha Allah zan san yadda zan yi na saka a fitar da saniya ɗaya sai a kai ta kasuwa a sayar, hakan ya yi miki?"
"Yawwa ko kai fa"
Janyo shi ta yi jikinta tana wani kanne masa ido ta ce, "Yau akwai bidiri a gidan nan tun da ka yarda da shawara ta hakan ya yi maka daɗi?".
"Fiye da tunaninki tawan." Ya faɗa cikin sassanyar murya. Murmushi kawai yake a fuska, amma zuciyarsa kuwa ji yake kamar za ta fashe tsabar ɗaci da kuma ƙunar da kalaman ta suka haifar masa. Sanin cewa yin fushi ko kuma nuna mata iyakarta ba shi ne masalaha ba, shi ya sa ya daidaita natsuwarsa kamar babu komai a ransa. Ya ɗan saki fuska ya ce,
"Tawan kin tabbata idan har na riƙa sayar  za ki riƙa ba ni kulawa ko?"
"Kulawa ta sosai ma kuwa rabin raina ina mai tabbatar maka sai ka saka hannu a ka ka yi ihun shelar babu wadda ta kai matarka ba wa mijinta kulawa cikin garin nan, wannan alƙawarina ne."
"Ni kuma zan yi miki duk abin da kike da buƙata amma fa kin san abin sai da dabara dan kuwa wancan tsohon akwai shegen wayo kamar dila dole sai mun yi taka-tsantsan. Ki yarda da ni da ɗaiɗai sai na ƙarar masa da garkensa baki ɗaya."
"Yawwa wannan shi ne mijin da nake burin kasancewa da shi, na gode maka sosai da ka fahimce ni. Yanzu dai kar ka fita tsaya mu ci wannan kazar tare kuma ina da kuɗi zan ba ka sai ka ƙaro mana wata ka ji!"
"Da dai kin ci kawai ni saina fita na sayo garin rogo"
"A'a kawai ka zauna mu ci wannan"
Haka kuwa ya zauna suka ci tare, yana gamawa ya ce, "Tawan bari na je na yi salla ke ma ki yi kafin na dawo kin ji shalelena?"
"Yanzu kuwa ai duk abin da ka ce babu musu" Yana fita ta daka tsalle tana cewa, "Sakarai wallahi Najibu har duniya ta naɗe ba na fatan Allah ya nuna mini ranar da zuciya ta za ta kamu da cutar son ka. Domin kuwa ita ce cuta mafi hatsari a rayuwata. Da za ka san irin tsanar da ke tsakanin zuciya ta da taka Wallahi da idan za a ba ka komai na duniyar nan ba zan taɓa yarda na zauna da kai na tsawon rayuwata ba. Banza shashasha, kalle ni fa har yaushe da kyawuna zan zauna cikin wannan ƙauyen wai da sunan aure? Tabbas na san cewa haihuwa ta da aka yi a nan ba ni da zaɓi, amma aure kam sai abin da na zaɓa wa kaina. Dan haka daga yau ka ma fara ƙirga ragowar ranakun da suka rage mana a tare mtssss!"
Wani irin kuka mai ƙuna ya saki bayan faifan kunnuwansa sun yi gangancin taimakon naɗar duk bayananta. Da ma ya san hakan za ta kasance, shi ya sa ya maƙele a bakin zauran gidan domin jin abin da za ta faɗa bayan wucewarsa. Ganin kukan ba shi da wani amfani sai ya nufi masallaci. Bayan ya idar ya zauna yana kan kukansa ga Wanda Shi kaɗai ne zai masa magani. Buɗe zuciyarsa ya yi sosai ya miƙa Wa Allah lamuransa, tare da yaƙinin Allah zai kawo masa mafita cikin wannan lamari. Daga nan kuma ya nufi gidan iyayensa. A zaune mahaifinsa yake yana goge baki da asuwaki. A gefe ɗaya kuma matarsa ce wato mahaifiyar Najibu wadda aƙalla za ta kai shekaru arba'in da bakwai kasancewar tana da kyawun jiki hakan ya sa idan ba an faɗa maka ba ba za ka taɓa fahimtar haka daga tsarin zubin da Allah ya yi mata ba. Ya samu wuri ya zauna. Tunda ya zauna bai ɗago kansa ko sau ɗaya ba, haka kuma bai furta ko kalma ɗaya ba. Yana ta saƙe-saƙe a zuciyarsa. Ban da hawaye babu abin da yake wanda gabaɗayan sa zuba suke kan kafar mahaifin nasa, saboda kusancin da ke tsakinsu in da ya sunkuyar da kan nasa da kuma ƙafar mahaifin nasa. Duk su biyun babu wanda ya yi ƙoƙarin hana shi ko kuma tambayar shi dalili don kuwa duk sun san cewa wannan halin sa ne tun lokacin ƙuruciya. Haka yake gudanar da rayuwarsa da zarar ya yi fushi to fa abu ɗaya ne yake gusar masa da ɓacin ransa, wato zama kusa da mahifinsa. Sai da ya gama sannan Malam Ali wanda a yanzu suke kiransa da Abba ya yi mata nuni da ta kawo masa ruwa, ruwa mai sanyi ta ɗebo ta kawo masa cikin ƙwarya mai tsafta. Miƙa masa ya yi ai kuwa cikin sauri ya karɓa ya kafa kai bai cire ba har sai da ya gama shanyewa tas sannan ya miƙa mata ƙwaryar yana cewa.
"Nagode Mimah."
Gyaran muryar mahaifinsa ya yi ya ce "Idan ban mance ba na nuna  maka in da maganin damuwarka take. Kuma ina da tabbacin ba ka mance ba, idan har ba ka mance ba me ya sa ka zo nan? Ka sani, ni da kai da kuma mahaifiyarka da ma kowane ne babu wanda zai iya magance maka matsalarka face Ubangijin da ya halicce ka, dan haka gurinsa kawai za ka miƙa kukanka ya kuma amsa maka babu shamaki, muddun addu'arka ba ta ƙarbu a lokacin da kake buƙata ba, ina mai tabbatar maka Allah ya fi ka sanin abin da ya fi zama alkairi a kan wannan buƙata taka. Sai dai kuma ka kasance mai lura da al'amurra yau da kullum, dan kuwa lamarin duniya ya wuce in da kake tunani. Wasu abubuwan samuwarsu a gare mu jarabawa ce mai zaman kant. Kuma idan muka yi haƙuri kuma muka miƙa wa Allah lamuranmu sai mu wuce ba tare da mu kanmu mun san lokacin ba, saboda haka ka yi haƙuri ka yi hakuri kuma ka ƙara hakuri tashi ka tafi Allah ya yi maka albarka." 
"Amin, Allah ya ƙara girma"
Da haka ya nufi gida, da murnarta ta ce. "Ina kuma ka tafi bayan ka san na faɗa maka akwai tukuici mai girma da zan yi maka ko dai ba ka so ne?"
"Tsayawa na yi saboda na yi sallar isha'i kafin na shigo"
Allah cikin ikonsa kafin wasu mintunan ya ji babu wani sauran ɓacin rai a tattare da shi. 

*SAFNAH ALIYU JAWABI*
(His Noor)

Post a Comment

Previous Post Next Post