RMC Hausa
LIVE Radio

WANKA MAZA DA MATA

AN KAMA MAZA DA MATA MASU WANKA A WAJE DAYA

Hukumar Hisba a Kano sun samu nasarar kamo wasu matasa su 20, da ake zargin suna Chashewa da kuma wanka Maza da Mata a wuri guda.

Dakarun Operation Kauda Badala ne, suka Kai sumamen a MRA SPORT & MORE, dake Ring Road , bayan samun korafe-korafen jama’a kan yadda Maza da Mata suke yin abubuwan da suka Saba da shari’ar addinin musulinci.

Mukaddashin Babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce dokar jahar ce ta Hana haduwar Maza da Mata, a cikin ruwa suna wanka a waje daya.

Dr. Mujahiddin Aminuddin , ya bayyana takaicinsa bisa samun Matasan da aka yi, a lokacin da yakamata ace suna yin zikirin juma’a da Neman gafarar Allah, tare da karanta alkur’ani mai girma.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa , Matasan da ake zargi sun shirya bikin Faty ,inda za a yi wanka Maza da Mata tsirara a cikin ruwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post