RMC Hausa
LIVE Radio

SANATA ƳAR ADDU'A YA BA MATASA KWAMFUTOCI KYAUTA

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya cika alkawalin da yaima wasu matasa na basu sabuwar kwamfuta laptop da kudi don inganta harkokin neman su da habaka karatun su da ayyukan su na yau da kullum.

Jiya ne Wakilin Sanata Alhaji Abu Bala Saulawa ya damka masu wadanan kwamfutocin a ofishin Sanatan na tuntuba dake cikin garin Katsina.

Matasan sun bayyana godiyar su bisa wannan abun arziki da kuma nuna halin dattako na fada da cikawa, Sunyi fatan Allah ya maimaita masa kujerar sa cikin yarda da amincin Allah.

Sen. Abdu Soja Media Team.

Post a Comment

Previous Post Next Post