*ADADIN FALASDINAWAN DA AKA KASHE A GAZA*
Watanni kusan bakwai kenan Isra'ila ta kwashe tana luguden wuta a Gaza kuma hakan ya sa gine-ginen da ta rusa sun kai nauyin kimanin tan miliyan 37.
Bayanai sun nuna cewa za a shafe shekaru da dama kafin a iya kawar da ɓaraguzan gine-ginen da hare-haren Isra'ila suka tara a yankin.
Kawo yanzu dai dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 34,622 tun da suka ƙaddamar da hare-hare ranar 7 ga watan Oktoba.