RMC Hausa
LIVE Radio

MA'AIKATA A SOKOTO SUN DARA

Da Ɗumi-Ɗuminsu daga RMC 

A yanzu haka mai girma gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu Sokoto, PhD, FCNA ya bayar da goron sallah ga ilahirin ma'aikatan jiha da na ƙananan hukumomi da kuma fansho da kuma masu karɓar alawus a ƙananan hukumomi da kuma hukumar kula da lafiya a matakin farko a faɗin jihar nan.

Rukunin farko ya haɗa da ma'aikatan jiha dana ƙananan hukumomi waɗanda suka karɓi naira dubu talatin N 30,000 kowanensu a matsayin goron sallah.

Sai kuma rukuni na biyu waɗanda ya haɗa da masu karɓar fansho da alawus a ƙananan hukumomi da ma su karɓar alawus a hukumar kula da kiyon lafiya a matakin farko wanda za su karɓi naira dubu Ashirin kowannensu N20,000.

Rukayya Ibrahim Lawal Daga Sokoto RMCHAUSATIMES

Post a Comment

Previous Post Next Post