HON. AMINU BALELE KURFI (ƊAN AREWA) YA KAWO HASKE A DUTSIN-MA
Gizawa • Fagguwa • Karofi • Bagaggadi • Dagon Zoo • Sabuwar Hanya.
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dutsin-Ma da Kurfi, Hon. Aminu Balele Kurfi (Dan Arewa), ta hannun wakilcin Shugaban Karamar Hukumar Dutsin-Ma, Hon. Kabir Abdulsalam Shema, ya kaddamar da aikin saka fitilun hanyoyi masu amfani da hasken rana (Solar Street Lights) a garin Fagguwa, tare da bayyana cewa aikin zai shafi garuruwan Karofi, Gizawa, Bagaggadi, Dagon zoo, Sabuwar Hanya da sauran unguwanni da ke cikin Karamar Hukumar.
A yayin jawabinsa, Shugaban Karamar Hukumar ya yabawa Hon. Aminu Balele Kurfi bisa tsayuwarsa tsayin daka wajen tafiyar da siyasar “alkawari aiki ne”, yana mai jaddada cewa aikin zai taimaka matuƙa wajen kara tsaro, walwala da kuma bunkasa tattalin arzikin al’umma.
Al’ummar yankunan da abin ya shafa sun bayyana matukar jin dadinsu da gamsuwa, tare da mika godiya ga Mai Girma Dan Majalisar Tarayya, suna mai bayyana aikin a matsayin sahihiyar shaida ta shugabanci mai aiki, kusanci da jama’a, da kishin ci gaban al’umma.
Taron kaddamarwar ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar APC, masu gari, masu unguwanni da dimbin magoya baya.
Kado Lawal Nura
Media Secretary General
To Hon. Aminu Balele Kurfi (Dan Arewa)
03/02/2026
RMC HAUSA
Category
Siyasa