RMC Hausa
LIVE Radio

KASIPA TA YI TARO A KATSINA

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ya ƙaddamar gagarumin taron masu ruwa da tsaki na Arewa maso yamma kan shirye-shiryen bada tallafi na gwamnatin tarayya 

...............Gwamnatin Tarayya tace ta kashe fiye da biliyan 30 wajen tallafawa al'ummar jihar Katsina 

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruq Lawal Joɓe ya ƙaddamar taron masu ruwa da tsaki na jihohin Arewa maso Yamma kan shirye-shiryen bada tallafi na gwamnatin tarayya da kuma ƙara adadin mutanen da za su ci gajiyar tallafi a ƙananan hukumomin 5 wanda yanzu duka ƙananan hukumomi na amfana da tallafin gwamnati.

Taron dai Hukumar kula da shirye-shiryen tallafi ta jihar Katsina KASIPA ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mudassir Nasir da hukumar ta kasa NSIPA haɗin gwiwa da United Nations World Food Programme UN-WFP suka gudanar da shirin.

Taron ya samu halartar manyan jami'an hukumar NSIPA daga hukumar ta ƙasa da Shugabannin hukumomin shirin na jihohin Arewa maso yamma da sauran manyan jami'ai da sauran su.

Malam Faruq Lawal Joɓe yace ɓullo da wannan taro, ya nuna irin jajircewar gwamnatin tarayya na tallafawa al'umma a faɗin ƙasar, ƙarƙashin ƙudirin shugaban ƙasa na Renewed Hope Agenda.

Mataimakin Gwamnan Jihar yace shirin ya taɓa rayuwar al'umma, wanda irin wannan taro zai taimakawa wajen gano yadda za'a ƙaddamar da shirin domin amfanar al'umma a faɗin ƙasar.

Shugaban Hukumar kula da shirye-shiryen tallafawa al'umma na gwamnatin tarayya, Farfesa Badamasi Lawal Charanci wanda ya samu wakilcin Abdullahi Imam ya bayyana cewa, daga cikin biliyoyin nairori da gwamnatin tarayya ta ware domin tallafawa al'umma, jihar Katsina ta amfani da Biliyan 30.

Farfesa Badamasi Lawal Charanci ya ce shirin zai karaɗe ko'ina a faɗin Nijeriya, kasancewar yanzu gwamnati na shirin biyan kuɗin Ma'aikatan da suka yi shirin N-Power domin biyan su haƙƙokin su.

A jawabin sa, Shugaban KASIPA Farfesa Mudansir Nasir ya ce a ƙoƙarin da Gwamna yake yi, ya sanya yanzu haka dukkanin ƙananan hukumomin 34 suna cin gajiyar shirin a faɗin jihar.

Farfesa Mudansir Nasir ya ƙara da cewa, an tallafawa dubban al'umma a ƙarƙashin hukumar kama da masu ƙananan sana'o'i da Malaman addini, da marasa ƙarfi da al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post