Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da matakin gwamnatin Amurka na kakaba takunkumi kan wani ɗan kasuwar Najeriya, Mukthar Muhammad Adamu, da wasu masu kamfanonin canji guda biyu bisa zarginsu da hannu wajen samar da kuɗaɗen tallafa wa ayyukan ta’addanci.
A wata sanarwa da sashen leken asirin kuɗaɗe na Najeriya (NFIU) ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana matakin da Amurka ta ɗauka a matsayin wani gagarumin ci-gaba a ƙoƙarin haɗin gwiwa na dakile matsalar tsaro.