RMC Hausa
LIVE Radio

NEMAN TAKARAR GWAMNA

ƊIYAR TSOHON SHUGABAN ƘASA ZA TA TSAYA TAKARA 

Farfesa Iyabo Obasanjo, ’yar tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Ogun a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki.

Ta bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata tattaunawa a shirin rediyo na Eagle 7 Sports a gidan rediyon 103.7FM, wanda fitaccen tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya, Segun Odegbami, ke gabatarwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Iyabo ta koma harkokin siyasa bayan shafe kusan shekaru 15 ba ta cikinta, inda ta shiga jam’iyyar APC domin shirye-shiryen zaɓen 2027 a Jihar Ogun.

Majiyoyi sun ce Iyabo, wadda ta wakilci mazabar Ogun Central a Majalisar Dattawa tsakanin 2007 zuwa 2011, ta halarci rajistar sabbin mambobin APC da ake yi a Ibogun, Ward 11, ƙaramar hukumar Ifo, wanda hakan ya tabbatar da shigarta jam’iyyar a hukumance.

Iyabo, wadda ƙwararriyar masaniya ce a fannin cututtuka kuma tsohuwar Kwamishinar Lafiya ta Jihar Ogun, ta sha kaye a zaɓen sake tsayawa takara a 2011, inda Sanata Gbenga Obadara na jam’iyyar ACN ta wancan lokaci ya kayar da ita. Daga bisani ta koma Amurka domin ci gaba da aikinta na ilimi, inda ta kai matsayin Farfesa.

Da take magana yayin hirar, tsohuwar Sanatar ta ce ta koma siyasa ne sakamakon matsin lamba daga magoya bayanta.

Ta ce, “Wasu mutane da ban kafa ƙungiyarsu ba, sun shafe kusan shekaru biyu suna aiki tare, sannan suka fara roƙona na dawo siyasa, suna cewa ni ce mafi dacewa da takarar.”

Iyabo ta ce ba za ta iya komawa jam’iyyar PDP ba, inda ta taba tsayawa takara, saboda rikice-rikicen da ke cikinta. Ta kuma bayyana cewa ta yi la’akari da jam’iyyar ADC, amma har yanzu ba ta shirya sosai ba.

Ta ƙara da cewa yawancin mutanen da suka roƙe ta ta dawo siyasa suna cikin jam’iyyar APC, kuma ta yi shawarwari da dama kafin yanke shawarar shiga jam’iyyar.

“A ganina APC ita ce gidana na siyasa. Ina jin daɗin kasancewa a cikinta, kuma na gamsu da shawarar da na yanke,” in ji ta.

Game da burinta na siyasa, Iyabo ta ce ba ta da niyyar komawa Majalisar Dattawa ko zama Kwamishina, illa kawai ta tsaya takarar gwamna.

Ta ce, “Abin da kawai zan dawo siyasa domin yi shi ne takarar Gwamna. Mun fara wannan tafiya, kuma za mu ci gaba da ita har zuwa ƙarshe. Muna da cikakken ƙuduri da jajircewa wajen ganin mun cimma wannan buri.”

RMC HAUSA

Post a Comment

Previous Post Next Post