A daren jiya alhamis 18-04-2024, ɓarayin daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suka kai hari ƙauyen Zamfarawar Madogara dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Ɓarayin sun kai samame a ƙauyen na Zamfarawa kuma sun kwashi jimillar mutane mata, maza da yara ƙanana har ashirin da takwas, 28, kamar yadda wani mazaunin garin ya bayyana ma wakilinmu, kuma sun kora su daji. Har ya zuwa haɗa rahotonnan ba'a ji ɗuriyarsu ba. Katsina city News ta wallafa labarin.