Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami'ar Tarayya ta Kimiyyar Lafiya, Azare, Jihar Bauchi, domin girmama marigayi malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Shugaba ya sanar da hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan malamin a gidansa da ke Bauchi, yana mai bayyana cewa an yanke shawarar ne domin adana tunawa da shahararren malamin da ya bada gudummawarsa ga al'ummma da kuma ilimin addini.
Da yake sanar da wannan sauyi, Tinubu ya ce daga yanzu za a kira wannan jami'a da Jami'ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yana mai bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga al'umma. Ya lura cewa an san Sheikh Dahiru Bauchi da tawali'u, hidimar al'umma, jajircewarsa wajen inganta zaman lafiya, da hadin kai.
Shugaba ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin malamin da kuma shigarsa Jannatul Firdausi, Ya kuma yi addu'ar Allah ya ba da hakuri ga iyali, da kuma gwamnati da mutanen jihar Bauchi, don jure rashin, yayin da ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da addu'ar zaman lafiya da hadin kan kasa.
Da yake jawabi a madadin iyalan, babban ɗan marigayi malamin addinin, Sheikh Ibrahim Usman Bauchi, ya nuna godiyarsa ga Shugaban ƙasa kan ziyarar ta'aziyya, addu'o'i, da kuma girmamawa da aka yi wa mahaifinsu. Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, bisa goyon bayan da yake bai wa iyalin a kowane lokaci.
A cikin jawabinsa, Gwamna Mohammed ya yaba wa Shugaban ƙasa kan girmama iyalin da kuma Jihar Bauchi, yana mai bayyana sauya sunan jami'ar a matsayin girmamawa da ta dace ga tarihin Sheikh Dahiru Bauchi.
Shugaban ƙasa ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni; Seyi Tinubu; da sauran manyan jami'an gwamnati.