Taron Sada Zumunci na Facebook Connect, ya tara Mutane daga sassan jihar Katsina da dama
Lokacin da ake ci gaba da taron, an tattauna abubuwan daban-daban kan kafafen sadarwa da al’adun Hausawa wanda ya haɗa mutane da dama a Taron Facebook Connect.
Ana ci gaba da gudanar da taron Katsina Facebook Connect karo na Shida a birnin Katsina, inda masana da masu ruwa da tsaki ke zurfafa nazari kan tasirin kafafen sadarwa na zamani wajen ingantawa ko gurbata al’adun Hausawa.
Katsina Post ta samu cewa, taron wanda ke gudana a ɗakin taro na Continental Computers Katsina, na ƙara jan hankalin mahalarta yayin da ake gabatar da kasidu masu ma’ana daukar hankali.
A farkon zaman, Dr. Mustapha Shehu, PhD, ya gabatar da jawabin gabatarwa, inda ya yi nuni da cewa kafafen sada zumunta sun buɗe sabon babi ga al’adun Hausawa, yana mai cewa za su iya zama kayan kare asali ko kuma hanyar lalata shi, gwargwadon yadda aka yi amfani da su.
Haka kuma, Farfesa Sani Audu Fari ya gabatar da jawabin maraba, inda ya bayyana cewa Katsina Facebook Connect 6.0 ya zama wani muhimmin dandali na shekara-shekara da ke haɗa ilimi, al’adu da fasaha a wuri guda.
Kasidar farko da Aliyu Idris Mai Kaji ya gabatar ta yi dubi kan rayuwar Hausawa a wannan zamani, musamman yadda al’adu ke fuskantar sauye-sauye sakamakon yawaitar amfani da kafafen sadarwa.
Baya ga kasidu, taron ya samu armashi ta hanyar wakar baka “Hanjin Jimina,” wadda ta isar da saƙonni masu zurfi kan tarbiyya, hikima da muhimmancin kiyaye al’adun gargajiya.
Taron dai na ci gaba da gudana cikin nutsuwa da birgewa, tare da ƙarin kasidu da baitoci masu daukar Hankali. Wannan ne karo na shida da ake gudanar da taron, wanda ke gudana duk shekara, lamarin da ke ƙara tabbatar da muhimmancinsa a fagen al’adu da sadarwa.
Category
Labarai