RMC Hausa
LIVE Radio

MAJALISAR SARAKUNA

Gwamna Raɗɗa Ya Ƙaddamar Da Majalissar Sarakuna Ta Jihar Katsina 

A ranar Talata 16 ga watan Disambar 2025, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya ƙaddamar da Majalisar Sarakunan Jihar Katsina, a fadar gwamnatin jihar Katsina.

A lokacin ƙaddamar da majalissar Gwamna Raɗɗa ya bayyana samar da majalissar a matsayin wani shafi da zai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya, domin cigaban jihar Katsina.

Gwamnan ya sanar da cewa Sarkin Katsina shi ne Shugaban Majalisar, yayin da Sarkin Daura zai zama Mataimakin Shugaba, Majalisar ta ƙunshi manyan hakimai da wakilai daga masarautun Katsina da Daura, tare da wakilan addini, kasuwanci da matasa, Sanata Ibrahim Mohammed Ida (Wazirin Katsina) shi ne Sakataren majalissar, yayin da Sada Salisu Danwairen Katsina yake Mataimakin Sakatare.

A cewar Gwamna Radda, Majalisar za ta ba gwamnati shawara kan harkokin shari’ar Musulunci da ta gargajiya, al’adu, sarauta, zaman lafiya, tsaro, da dangantakar al’umma, tare da tallafawa ci gaban al’umma da kare muhalli.

Gwamnan ya taya mambobin Majalisar murna tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon gudanar da ayyukansu domin cigaba da zaman lafiyar Jihar Katsina.
RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post