An gudanar da taron horaswa na yini guda ga dalibai da matasa kan yadda za su yi amfani da fasahar kirkira (AI) wajen karatu da bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) a jihar Katsina.
Hukumar Bada Tallafi da Bunkasa Rayuwar Al’umma ta Jihar Katsina (KASEPA), karkashin shirin GEEP, ta shirya taron ne domin ilmantar da matasa akan amfani da fasahar kirkira wajen tallata kasuwanci da kuma taimakawa wajen gudanar da karatunsu.
A ranar Laraba, 17-12-2025, Shugabar Shirin GEEP ta Jihar Katsina, Hajiya Karima Abdulkarim, ta jagoranci kaddamar da taron horaswar na yini guda ga dalibai a Makarantar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina (KSITM), dake cikin garin Katsina.
A jawabin da ta gabatar, Shugabar Shirin GEEP, Hajiya Karima Abdulkarim, ta bayyana cewa wannan taron wani bangare ne na kokarin Gwamnatin Jihar Katsina na karfafawa dalibai da matasa wajen inganta ilimi da habbaka sana’oi.
Ta kara da cewa, hukumar za ta ci gaba da bada gudunmuwa wajen wayar da kan dalibai da matasa akan hanyoyin zamani na karatu da habbaka sana’oi, musamman ga masu kananan masana’antu.
Hakazalika, Mai Taimakawa Gwamna akan Harkokin Dalibai, Hon. Muhammad Nuhu Nagaske, ya yi jawabi inda ya yi kira ga dalibai da su maida hankali wajen koyon sabbin dabaru da ake amfani da su domin samun sauki a bangaren karatu da kuma hanyoyin tallata kasuwanci.
Dr. Mustapha Shehu, wanda shima ya yi jawabi a wurin taron, ya yi kira da shawartar daliban akan muhimmanci da amfanin fasahar AI wajen bincike da karatu.
Taron ya samu halartar Shugaban Hukumar KATDICT Naufal Ahmad, Shugaban kamfanin kafar sadarwa na mobile media crew Alh. Abubakar Shafi'i, Hajiya Amina Abdulkarim, manya manyan Bak, Shugaban kungiyar Matasa ta Kasa reshen jihar Katsina ( NYCN) Yusuf Abubakar, dalibai da dai sauransu.
Mmc