RMC Hausa
LIVE Radio

BIKIN MAULIDIN SHEHU

Birnin Katsina Ta Dinke Dif Yayin da Ake Cigaba Da Shirye-shiryen Bikin Mauludin Ƙasa Da Kasa na Sheik Ibrahim Inyass

Birnin Katsina ta cika makil da al’umma daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashe makwabta, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da gagarumin bikin Mauludin Ƙasa na Sheik Ibrahim Inyass.

Tuni masoya da mabiya darikar Tijjaniyya suka mamaye manyan tituna da masaukan birnin, inda ake hasashen cewa mafi yawansu za su kwana ba tare da bacci ba, sakamakon ci gaba da zikiri, karatuttuka da tarurrukan addini da suka haɗu da bikin.

Hukumomin tsaro da na kula da zirga-zirga sun kara ƙaimi wurin tsare-tsare domin tabbatar da tsaro da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a a yayin taron.

Ana sa ran bikin zai samu miliyoyin mahalarta daga dukkan faɗin duniya.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post