RMC Hausa
LIVE Radio

GIDAUNIYAR LAMIƊO

Naira Milyan 1,000,000 da katan 200 na lemu da ruwa Gidauniyar Lamido Foundation ta bada gudunmuwa ga kwamitin shirya Maulidi Shehu Ibrahim Inyass a jahar Katsina. 

A ranar Litinin 12/01/2026, Gidauniyar ta lamido ta hannanta kudin da lemunan ga shugaban kwamitin shirya Maulidi Sheik Hadi Balarabe.

Da yake gabatar da jawabin shi kafin hannanta gudunmuwar Alh. Bishir Dan Gambo ya bayyana cewa" shugaban Gidauniyar Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri yaso ya hannata gudunmuwar dad kanshi.

Amman duba da yana yin aiki yasa bai zoba, ya bada umarni da a hannata gudunmuwar ga kwamitin shirya Maulidi.

Daga karshe ya bukaci a kara sanya jihar Katsina cikin addu'a, kuma Allah yasa ayi taro lafiya a gama lafiya.

A nashi jawabin Sheikh Hadi Balarabe ya nuna godiyarshi matuka bisa gudunmuwar, inda ya bayyana cewa" Allah ya sakama Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri da mafifincin alheri, Allah ya biya ma shi dukkan bukatun shi na alheri.

Daga karshe ya tabbatar ma wanda suka hannanta gudunmuwar cewa" insha Allah za'a sanya Hon Jabiru Salisu Abdullahi a cikin dukkan addu'o'in da ake yi da niyar Allah ya biya masa dukkanin bukatun shi.

Daga cikin wanda suka taimaka wajen hannanta gudunmuwar akwai Sakataren ƙaramar hukumar kurfi Hon Mustapha, Shugaban kamfanin Mobile Media Crew Alh. Abubakar Shafi'i, tsohon shugaban babbar kasuwar Katsina Abbas Labaran Albaba da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post