Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kansa a matsayin muƙaddashin shugaban ƙasar Venezuela, kwanaki kaɗan bayan ya kai hari ƙasar inda aka kama Shugaba Nicolas Maduro aka tafi da shi Amurka.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya nuna kansa a matsayin muƙaddashin shugaban ƙasar da ke Kudancin Amurka daga watan Janairun 2026.
A makon jiya ne Trump ya ce daga yanzu shi ne zai riƙa juya kuɗin man fetur na Venezuela.
Trump ya ce Amurka za ta karɓi gangar ɗanyen mai miliyan 30 zuwa 50 daga gwamnatin wucin-gadi ta Venezuela kuma a riƙa sayarwa a farashin kasuwa.
"Za a sayar da man da za mu karɓa daga Venezuela a farashin kasuwa, kuma ni da kaina, a matsayina na shugaban Amurka, zan riƙa juya ribar da aka samu," in ji shi.
RMC HAUSA